ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters daga birni Nairobi inda ofishin hukumar reshen nahiyar Afrika ya ke, ya kara da cewa idan an samar da alluran sai har yi gwajinsa a nahiyar ta Afirka kafin a fara yi wa mutane.
Reuters ya nakalto Richard Mihigo shugaban hukumar ta WHO a nahiyar Afirka ya na fadar haka a jiya Alhamis ya kuma kara da cewa wannan adadin shi ne kashi 20% na yawan mutanen Afirka, sannan za’a fara yiwa jami’an kiwon lafiya alluran riga kafin don su ne a gaba-gaba wajen yaki da cutar, sannan a fara yi wa sauran mutane.
Labarin ya kammala da cewa ya zuwa yanzu dai alluran guda biyu ne kawai aka fara gwajinsu a nahiyar afirka.
342/